Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan sandan Hong Kong sun tsare mutane 5 bisa cin mutuncin tutar kasa
2019-08-16 14:21:12        cri
Rundunar 'yan sandan Hong Kong ta ce ta kama mutane 5 da ake zargi da cin mutuncin tutar kasa.

An kama mutanen 5 da suka hada da maza 4 da mace 1 masu shekaru tsakanin 20 – 22 ne a ranekun 14 da 15 ga watan Agusta a yankunan Mong Kok da Ma On Shan da Sham Shui Po da Ngau Tau Kok da kuma Wong Tai Sin.

'Yan sandan sun kuma kwace kwamfutoci da wayoyi da tufafi daga gidajensu domin ci gaba da bincike.

A ranekun 3 da 5 ga watan nan, wasu masu zanga-zanga suka cire tutar kasar Sin daga jikin sandarta a yankunan Tsim Sha Tsui da Kowloon, daga bisani kuma suka jefa cikin teku. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China