Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta mayar da martani kan kalaman Amurka game da batun Hong Kong
2019-08-17 16:39:02        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bada amsa kan tambayar da dan jarida ya yi mata a jiya 16 ga wata kan wasu kalaman Amurka game da batun Hong Kong.

Wani dan jarida ya yi tambayar cewa, "an labarta cewa, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya furta cewa, idan shugabannin kasar Sin sun gana da masu zanga-zanga, to batun Hong Kong zai samu wani sakamako mai kyau. Wato Trump na son ganin Sin ta daidaita batun Hong Kong ta hanyar jin kai. Ina ra'ayin Sin kan batun?"

Madam Hua ta amsa cewa, tun bayan watan Yuni na bana, laifuffukan nuna karfin tuwo da aka aiwatar a yankin Hong Kong suna ta tsananta, lamarin da ya karya doka da odar zamantakewar al'ummar wurin, kana ya kawo babbar illa ga zaman karko da wadatar Hong Kong, da ma bata manufar "kasa daya, tsarin mulki biyu". Aikin dake sama da komai yanzu shi ne kwantar da kurar da ta tashi a yankin bisa doka, da ma mayar da oda yadda ya kamata.

Hua ta jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan goyon bayan jagorar Hong Kong Madam Carrie Lam Cheng Yuet-ngor kan yadda take jagorantar gwamnatin yankin wajen tafiyar da harkoki bisa doka, da ma goyon bayan 'yan sandan Hong Kong wajen gudanar da aikinsu a tsanake, gami da goyon bayan hukumomin gwamnatin yankin da abin ya shafa da ma hukumomin shari'a wajen yanke hukunci ga masu aikata laifin. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China