Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bayyana ra'ayinta kan kalaman banza na 'yan majalisar dokokin Amurka game da batun Hong Kong
2019-08-17 20:29:08        cri

Yau Asabar 17 ga wata, You Wenze, kakakin kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar Sin ya bayyana cewa, lamuran tashin hankali masu tsattauran ra'ayi da suka faru a 'yan kwanakin baya a yankin Hong Kong na kasar Sin sun sabawa Kundin Tsarin Mulkin Kasar Sin, da Babbar Dokar yankin musamman na Hong Kong na Sin, da Dokar tutar kasar Sin, da Dokar alamar kasar Sin, da ma sauran dokoki da ka'idoji na yankin Hong Kong. Batun dai ya bata manufar "kasa daya, tsarin mulki biyu", kana ya kawo barazana ga rayuwa da dukiyoyin mazauna Hong Kong. Don haka dole ne a yanke hukunci ga masu aikata laifin bisa doka.

Kakakin ya fadi hakan ne domin mayar da martani kan kalaman banza da shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, 'yan majalisar dattijan kasar Mitch McConnell da Marco Rubio, da dan majalisar wakilan kasar Ted Yoho suka yi game da batun Hong Kong.

You Wenze ya kuma furta cewa, wasu 'yan majalisar Amurka sun mayar da batun tashin hankali da aikata laifi a matsayin yunkurin neman hakkin dan Adam da 'yanci, sun jirkita yadda 'yan sandan Hong Kong suke ta gudanar da ayyuka bisa doka, da yakar masu aikata laifi, da ma kiyaye odar zamantakewar al'umma a matsayin batun murkushe masu zanga zanga. Har ma sun kalubalanci majalisar dokokin Amurka da ta zartas da "dokar hakkin dan Adam da demokuradiyyar Hong Kong". Babu shakka lamarin da ya saba ruhun gudanar da harkoki bisa doka, kuma tsoma baki ne kan harkokin cikin gidan kasar Sin.

Ban da wannan kuma Mr. You ya ce, Hong Kong wani yanki ne na kasar Sin, harkokin Hong Kong harkokin cikin gida ne na kasar Sin. Zaman karko da samun wadata a Hong Kong cikin dogon lokaci aniya ce ta dukkan jama'ar Sin, ciki har da mazauna yankin Hong Kong miliyan 7.5, wadanda ba zai yiwu wasu masu amfani da karfin tuwo 'yan kalilan da wasu kasashen ketare za su iya sauyawa ba. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China