Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin ma'aikatar harkokin wajen Sin dake Hong Kong ya yi tir da hada kai da wasu 'yan siyasar Amurka ke yi da masu tsattsauran ra'ayi
2019-08-16 13:28:27        cri
Ofishin kwamishina na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin musammam na Hong Kong, ya yi tir da wasu 'yan siyasar Amurka dake hada kai da masu tsattsauran ra'ayi dake keta dokoki a Hong Kong.

Da yake mayar da martani ga jawabai marasa tsuhe da kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi da wasu 'yan siyasar kasar suka yi a baya-bayan nan dangane da yankin Hong Kong, kakakin ofishin ya ce wadannan 'yan siyasa na jirkita gaskiya da karya da nuna bangaranci da hada kai da masu tsattsauran ra'ayi dake keta dokoki, a wani yunkuri na tada rikici a yankin Hong Kong da ma kasar Sin baki daya.

Kakakin ya jaddada cewa, gwamnatin Sin da al'ummarta, jajirtattu ne wajen kare ikon mulkin kasa da tsaro da kuma muradun ci gaba.(Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China