Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta musanta tsokacin 'yan siyasar Amurka game da yankin Hong Kong
2019-08-14 09:39:25        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi watsi da tsokaci da dama na 'yan siyasar Amurka game da batun yankinta na Hong Kong, tana mai cewa, zantukan na su sun tauye gaskiya.

Rahotanni sun ce, kakakin majalisar wakilan Amurka Pelosi da Sanata Mc Connell da Sanata Rubio da kuma dan majalisa Yoho, sun wallafa a shafin Tweeter cewa, 'yan sandan Hong Kong sun yi amfani da karfi kan masu zanga-zanga, kuma gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta lalata tsarin demokradiyya da 'yancin yankin Hong Kong.

Kakakin ma'aikatar Hua Chunying, ta ce zantukan na su na wanke laifuka da sunan fafutukar hakkokin bil adama da yanci, kuma da gangan suke yi wa aikin 'yan sandan Hong Kong bahaguwar fassara a matsayin amfani da karfi kan masu zanga-zanga, bayan 'yan sandan na kokarin tabbatar da doka da oda da yaki da laifuka.

Ta kara da cewa, tsokacin na su ya sanya mazauna Hong Kong yin fito na fito da gwamnatin musammam na yankin da kuma gwamnatin tsakiya ta kasar Sin.

Hua Chunying, ta ce bangaren Amurka ya sha musanta cewa yana da hannu cikin rikicin dake faruwa a Hong Kong. Sai dai, wadancan tsokaci sun samarwa duniya sabuwar shaida mai kwari game da sa hannun kasar cikin rikicin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China