Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Xinjiang ta samu babban ci gaban tattalin arziki da ba a taba ganin irinsa ba a baya
2019-07-30 20:37:24        cri
A yayin taron manema labaru da ofishin watsa labarun majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya a yau Talata, shugaban jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur, Shohrat Zakir ya bayyana cewa, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa a jihar ko (GDP) a shekarar 2018, ya kai RMB triliyan 1.2, don haka ana iya cewa, jihar din ta samu ci gaban tattalin arziki da ba ta taba ganin irinsa ba a tarihi.

Shohrat Zakir ya kara da cewa, cikin shekaru 70 tun bayan kafa sabuwar kasar Sin, tattalin arzikin jihar Xinjiang ya samu babban ci gaba, kana zaman rayuwar jama'a 'yan kabilu daban daban dake jihar ya samu kayutatuwa sosai. A cewarsa, yawan GDPn jihar ya karu daga miliyan 791 a shekarar 1952, zuwa triliyan 1.2 a shekarar 2018. Ya ce idan ba a yi la'akari da dalilin karuwar farashin kayayyaki ba, adadin ya ninka har sau 200. Kaza lika matsakaicin karuwar adadin a ko wace shekara ya kai kashi 8.3 cikin 100.

Jihar Xinjiang ta kasar Sin dake tsakiyar babban yankin Asiya da Turai, cibiya ce kuma dake kan hanyar siliki. Tun bayan da aka tabbatar da ita a matsayin cibiya ta zirin tattalin arziki na siliki a shekarar 2014, jihar ta yi amfani da wannan fifikonta, da babbar dama ta raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", tana ta kokarin bude kofa, da nufin tabbatar da matsayin jihar na cibiyar zirin tattalin arziki na siliki, kuma kofar kasar Sin ga yammacin duniya.

A shekarar 2018, jimilar cinikayyar shige da fice ta jihar, ta kai dala biliyan 20, wadda ta ninka sau 1481, bisa abun da jihar ta samu a shekarar 1950. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China