Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe fiye da 50 sun nuna goyon baya ga manufofin Sin kan yankin Xinjiang
2019-07-29 21:37:39        cri
An ce, kasashe 24 membobin majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD, sun taba mika wasikar hadin gwiwa, don zargin manufofin Sin kan jihar Xinjiang. Amma a kwanakin baya, jakadun kasashe fiye da 50 sun mika wasikar hadin gwiwa ga shugaban majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD, da ofishin babban kwamishinan kula da kare hakkin dan Adam wato OHCHR, inda suka nuna goyon baya ga matsayin gwamnatin Sin kan batun jihar Xinjiang ta kasar.

Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta yi nuni da cewa, kasashe 24 da suka zargi kasar Sin, kasashen yammacin duniya ne masu ci gaba, kuma yawan mutanensu ya kai miliyan 600. Amma kasashe fiye da 50 masu goyon bayan kasar Sin, kasashe ne daga nahiyar Asiya, da Afirka, da Turai, wadanda yawan mutanensu ya kai kimanin biliyan 2, kuma kasashe 28 a cikinsu mambobi ne na kungiyar kasashe musulmi ta OIC. Ta hakan kuma ana iya gano wane ne ya fadi gaskiya game da batun Xinjiang. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China