Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin bankin duniya a Nijeriya na daga cikin shiryen-shiryensa mafi girma a Afrika
2019-08-09 10:31:23        cri
Shirin bankin duniya a Nijeriya, na daga cikin manyan shirye-shiryen da bankin ke aiwatarwa a nahiyar Afrika, wanda ya lakume kimanin dala biliyan 11.

Darektan bankin a Nijeriya, Rachid Benmessaoud ne ya bayyana haka a Abuja, babban birnin kasar, yayin bikin bada lambar yabo ta farko na bankin.

An shirya bikin ne domin jinjinawa irin kokarin da aka yi wajen aiwatar da shirye-shiryen bankin a matakan jihohi da na kasa baki daya.

Rachid Benmessaoud, ya bayyanawa mahalarta taron cewa, ana aiwatar da kaso 60 na shirye-shiryen bankin ne a matakin jiha da kuma kaso 40 a matakin gwamnatin tarayya.

Ya ce, bankin na da shirye-shirye sama da 30 dake gudana a kasar, inda ya ce abun da bankin ya kashe a Nijeriya ya kai dala biliyan 11. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China