Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A kalla 'yan Najeriya 200,000 ne ke rasuwa sakamakon cin abinci mai guba a duk shekara
2019-08-09 09:20:55        cri
Babban sakatare a ma'aikatar kimiyya da fasaha a tarayyar Najeriya Bitrus Nabasu, ya ce a kalla 'yan kasar 200,000 ne ke rasuwa duk shekara, sakamakon cin abinci mai guba, matsalar da kawo yanzu gwamnatin Najeriya ke kokarin shawo kan ta.

Mr. Nabasu ya bayyana hakan ne, yayin wani taron karawa juna sani game da kare ingancin abinci, wanda ya gudana a jihar Nasarawa dake shiyyar tsakiyar kasar, yana mai cewa a duk shekara a kasar wadda ta fi sauran kasashen Afirka yawan al'umma, ana samun bullar nau'ikan cututtuka kimanin 90,000 masu nasaba da cin abinci maras kyau.

Ya ce sau da yawa abinci na gurbata ne yayin da ake sarrafa shi, ko kuma ta hanyoyin alkinta shi. Domin shawo kan wannan matsala, jami'in ya ce ya zama wajibi hukumomin da lamarin ya shafa, kamar SON da hukumar NAFDAC, su kara azama wajen tabbatar da cewa, ana aiwatar da matakan kare ingancin abincin da al'ummar kasar ke amfani da shi a dukkanin matakai. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China