Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun tsaron Najeriya sun dakile yunkurin harin Boko Haram a wani kauyen jihar Borno
2019-08-08 11:05:43        cri
Wani babban jami'i ya bayyana a jiya Laraba cewa, jami'an tsaron Najeriya sun yi nasarar dakile wani harin da mayakan Boko Haram suka shirya kaddamarwa a ranar Talata a wani kauye dake jihar Borno a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan ya kai ziyara kauyen, inda ya ce wasu gungun mayakan Boko Haram sun yi yunkurin kutsawa kauyen Kotori dake karamar hukumar Konduga a jihar, sai dai jami'an tsaron da aka tura yankin sun dakile yunkurin maharan.

Gwamnan ya yabawa aniyar dakarun musamman na Operation Lafiya Dole wadanda suka dakile harin da aka shirya, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta karfafa gwiwa ga jami'an tsaron sa kai da maharba domin su tallafawa jami'an sojoji da sauran hukumomin tsaro a jahar.

Zulum bai yi karin haske game da wadanda suka samu raunuka ko mutuwa a sanadiyyar yunkurin harin daga bangarorin biyu ba, sai dai ya jaddada yin kira ga mayaka 'yan ta'addan da su gaggauta mika wuya, kana su ajiye makamansu domin rungumar shirin sauya tunani don sake mayar da su cikin al'umma.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China