Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU za ta kira taron tara kudi domin taimakawa tunkarar Ebola a DRC
2019-07-27 16:42:41        cri
Tarayyar Afrika AU, ta bayyana a jiya cewa, za ta kira taron samar da kudi, na bangarori masu zaman kansu na nahiyar da masu bada gudunmuwa, domin taimakawa aikin tunkarar cutar Ebola dake gudana a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

AU wadda ta jadadda matukar damuwarta kan batun yaduwar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ta bayyana a jiya cewa, za ta kira taron manyan jami'ai mai taken : "asusun hadin kai na Afrika, domin yaki da Ebola" a farkon makon watan Satumban bana, da nufin samar da abubuwan da ake bukata na tunkarar Ebola a nahiyar.

A cewar wasu alkaluma da tarayyar mai kasashe mambobi 55 ta fitar, ya zuwa ranar 18 ga watan nan, an samu rahoton mutane 2,532 da ake tsammanin sun kamu da cutar, kuma daga cikinsu an tabbatar da 2,438 sun kamu, sannan ana tababa kan ko mutane 94 sun kamu, baya ga 1,705 da suka mutu, da kuma 718 da suka warke, yayin barkewar cutar mafi girma na 2 a tarihi tun bayan gano ta a shekarar 1976.

Sanarwar da AU ta fitar jiya, ta ce ana sa ran taron wanda zai gudana karkashin shugaban hukumar kula da ayyukan tarayyar, Moussa Faki Mahamat, zai hada wakilan bangarori masu zaman kansu na fadin nahiyar da kuma abokan hulda da masu bada gudunmuwa na kasa da kasa.

Ko a baya ma, AU ta shirya taron samar da kudi na nahiyar a shekarar 2014 kan batun, a lokacin da Ebola ta barke a kasashen yammacin nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China