![]() |
|
2019-08-01 10:58:28 cri |
Cikin wata sanarwar da ta fitar, mambobin kwamitin kasashe 15 sun bayyana juyayi da ta'aziyya ga iyalan mutanen da harin ya rutsa da su, da kuma mutane da gwamnatin kasar ta yammacin Afrika.
UNSC ta yabawa kokarin da kasashen shiyyar karkashin tawagar dakarun hadin gwiwar wanzar da zaman lafiya na shiyyar, wadanda ke yaki da ayyukan ta'addanci, kana MDDr ta bukaci su kara azama wajen tabbatar da tsaron shiyyar.
Mambobin kwamitin sulhun sun yi tir da dukkan wani nau'in ta'addanci inda suka bayyana cewa shi ne barazana mafi tsanani ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
Haka zalika, kwamitin MDD ya bukaci a binciko wadanda ke da alhakin kaddamar da hare-haren, da kungiyoyin dake tallafa musu, da masu samar musu da kudade, don gurfanar da su a gaban shara'a, kana an bukaci dukkan jihohin su hada gwiwa da gwamnatin Najeriya da hukumomin da abin ya shafa don tabbatar da zaman lafiya da tsaro. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China