Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bayyana matukar damuwa game da yanayin barkewar annobar Ebola a DRC
2019-07-26 10:57:50        cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta bayyana matukar damuwa game da yanayin da ake ciki na barkewar cutar annobar Ebola a jamhuriyyar demokuradiyyar Kongo (DRC).

Wata sanarwa da AU ta fitar ta nuna cewa, cutar ta haifar da mummunar barazana ga zaman lafiya da tsaron kasar, da shiyyar, har ma da nahiyar Afrika baki daya.

Ya zuwa ranar 17 ga watan Yulin bana, cutar Ebolar ta yi sanadiyyar hallaka mutane 1,621 a DRC, wannan ita ce barna karo na biyu mafi muni da cutar Ebolar ta haddasa a tarihi tun bayan gano cutar a shekarar 1976.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) a makon da ya gabata ta bayyana barkewar cutar Ebolar a matsayin babbar barazanar lafiya ga al'ummar duniya wacce ke bukatar daukin gaggawa na kasa da kasa.

A taron da ta gudanar na baya-bayan nan, majalisar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta AU, ta tattauna game da halin da ake ciki na barkewar annobar cutar ta Ebola a gabashin DRC, inda ta bukaci a dauki matakan gaggawa domin dakile yaduwar cutar, kana a yi kokarin hana bazuwar cutar zuwa sauran sassan kasar da ma kasashen dake makwabtaka da DRC.

Majalisar ta kuma yi Allah wadai da hare-haren da aka kaddamar kan cibiyoyin kiwon lafiya da jami'an kiwon lafiya a gabashin DRC, majalisar ta bukaci kungiyoyin masu dauke da makamai a gabashin DRC da su gaggauta tsakaita bude wuta domin baiwa jami'an lafiya damar gudanar da ayyukasu, wanda ya shafi ceto rayuwar fararen hula.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China