Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wata makala ta nuna rashin gaskiyar Amurka game da kare hakkokin bil Adama
2019-07-26 13:32:27        cri

Kungiyar kare hakkokin bil Adama ta kasar Sin ko CSHRS a takaice, ta fitar da wata makala dake nuna rashin gaskiyar kasar Amurka, game da batun kare hakkin bil Adama, musamman a fannin nuna wariyar launin fata.

CSHRS ta ce, duk da cewa Amurka na ayyana kanta, a matsayin mai rajin kare hakkokin bil Adama, a zahiri take cewa, ba ta da nufi, ko iko na warware matsalar nuna wariyar launin fata dake wakana a cikin gidanta. Hakan a cewar makalar, ya nuna gazawar tsarin gudanarwar ta a wannan fanni.

Har ila yau, makalar wadda aka wallafa a jiya Alhamis, ta ce nuna wariyar launin fata ya karade daukacin sassan rayuwar Amurkawa, musamman ma fannonin shari'a, da kare doka, da tattalin arziki da zamantakewa.

An dai yi wa makalar taken "Zurfafar wariyar launin fata a Amurka na nuni ga rashin gaskiyar kasar game da batun kare hakkokin bil Adama."

A cewar makalar, wanzuwar wannan yanayi ya haifar da kazantar laifuka masu nasaba da nuna wariya, da na nuna kyama, da karuwar karya dokokin zamantakewa, wanda hakan ke tarnaki ga manufar samar da daidaito tsakanin al'umma, da kare 'yancin tsiraru a cikin al'umma.

Bugu da kari, mukalar ta bayyana cewa, matsayar Amurka game da batun kare hakkokin bil Adama, na dogaro ne ga salon gudanarwa kasar, da tarihinta, da kuma akidunta. To sai dai kuma muddin kasar ba ta aiwatar da sauye-sauye ba, ba za ta taba cimma nasarar magance matsalar nuna wariyar launin fata, da kare hurumin al'ummu marasa rinjaye ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China