Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka na zagaye na 12 a birnin Shanghai
2019-07-26 13:50:32        cri
Za a gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, zagaye na 12 tun daga ranar 30 zuwa 31 ga wannan wata a birnin Shanghai dake kasar Sin. Wasu kafofi na Amurka na cewa, Sin da Amurka na raba gari ta fannin tattalin arziki, game da haka, kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana a jiya a nan birnin Beijing cewa, idan har an yanke huldar tattalin arziki a tsakanin Sin da Amurka kamar yadda kafofin yada labaran suka fada, ta hakan ya saba tsarin kasuwanci, da burin kamfanoni, da bukatun jama'ar kasashen biyu, har ma zai kawo babbar illa ga tsarin sana'o'i, da tattalin arzikin duniya baki daya.

A cikin shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka, an kafa tsarin hadin gwiwa da dogaro da juna a tsakaninsu a fannin tattalin arziki, wanda hakan ya kawo moriya ga jama'ar kasashen biyu har ma ga dukkan duniya. Ya ce, ba a son ganin yanke huldar tattalin arziki a tsakanin Sin da Amurka, kana bangarori daban daban na kasar Amurka ba su son fuskantar hakan. Ana fatan wasu mutanen kasar Amurka za su yi watsi da ra'ayin yin takara a tsakanin kasa da kasa wadanda yawan ribar da suke samu ta yi daidai da yawan hasarar da sauran kasashe suke tabkawa, da kara gudanar da ayyukan amfanawa jama'ar kasashen biyu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China