![]() |
|
2019-08-10 20:43:11 cri |
Zhou Pingjian ya yi nuni da cewa, tsananta halin da ake ciki a yankin Hong Kong yana da nasaba da wasu 'yan siyasa na kasashen yammacin duniya musamman na kasar Amurka, wadanda suka zuga jama'ar yankin, wadanda suka nuna goyon baya ga masu tsattauran ra'ayi da masu tada rikici, manufarsu ita ce nuna adawa ga kasar Sin ta hanyar tada rikici a yankin Hong Kong.
Zhou Pingjian ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin ba ta amince wasu kasashe su tsoma baki kan harkokin yankin Hong Kong, da kuma tada rikici a yankin ba. (Zainab)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China