Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana adawa da yadda Amurka ke ci gaba da tsoma baki a harkokin Hong Kong
2019-08-09 20:12:41        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta sake yin kira ga bangaren Amurka, da ya gaggauta daina tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan Hong Kong da ma na kasar Sin.

Madan Hua ta yi wannan kira ne a Jumma'r nan, bayan da mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka a jiya Alhamis ta karyata rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka bayyana bayanan wani jami'in diflomasiyan Amurka da ya gana da masu fafatukar neman 'yancin yankin Hong Kong.

Hua ta ce, ya kamata kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta san kalaman dake fita daga bakinta da ma abin da take yi, sannan bai kamata ta yi amfani da rahotannin kafafen labarai tana dora laifi ko zargin gwamnatocin wasu kasashe ba.

Jami'ar ta kasar Sin ta ce, a baya-bayan nan bangaren Amurka yana ta tsoma baki a cikin harkokin yankin Hong Kong, wadda hakan ka iya haifar da adawa da ma harzuka al'ummar Sinawa, ciki har da 'yan uwa mazauna yankin Hong Kong。

Don haka, ta bukaci bangaren Amurka, da ya mutunta dokokin kasa da kasa da muhimmin ka'idojin da suka shafi alakar kasa da kasa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China