Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi watsi da kalaman son zuciya da jami'in Amurka ya yi kan shawarar BRI
2019-05-10 10:45:42        cri
Kasar Sin ta yi fatali da kalaman rashin dattakun da wani jami'in Amurka ya yi game da shawarar "ziri daya da hanya daya" wato (BRI) a takaice, Sin tana mai cewa kasashen duniya za su iya tantancewa wane ne ke neman jefa su cikin matsala da kuma wanda ke kokarin nuna bambanci.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, shi ne ya yi wannan tsokaci a taron 'yan jaridu a yayin amsa tambaya game da wani rahoton dake cewa a lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya kai ziyara Birtaniya ya ce shawarar BRI wadda kasar Sin ta gabatar da ita ta ci karo da dokokin ikon mallaka da sauran kasashen ke da shi, har ma ya bukaci Birtaniya da ta sanya ido kuma ta fito fili ta yi Allah wadai da shawarar.

"Wasu daidaikun mutane a Amurka suna ci gaba da yin munanan kalamai kan shawarar "ziri daya da hanya daya", wacce ta samu matsayin amincewa tun gabanin taron dandalin shawarar ta "ziri daya da hanya daya" karo na biyu na hadin gwiwar kasa da kasa.

"Amma mene ne sakamakon? Sama da wakilai 6,000 daga kasashen duniya 150 kana da kungiyoyin kasa da kasa 92 ne suka halarci taron dandalin, wanda ya kunshi wakilai sama da guda 50 daga kasar Amurka kadai, wadanda suka halarci taron dandalin, in ji kakakin na Sin.

Geng ya ce, wannan dai kasashen duniya ne suka dauki matakai bisa radin kansu inda suka kada kuri'ar amincewa da nuna goyon baya ga shawarar BRI, kuma wannan shi ne martani mafi dacewa ga kalamai da matakin Amurka. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China