![]() |
|
2019-08-01 10:31:20 cri |
Jami'in na UNDP ya bayyana hakan ne, yayin da yake yawabi a wani taron karawa juna sani da aka shirya a birnin Addis Ababan kasar Habasha, don tattauna wani aikin samar da ci gaba mai dorewa da makamashin da ake sabuntawa, shirin da kasashen Habasha da Sri Lanka da kasar Sin za su gudanar tare.
Ya ce, gudummawar da kasar Sin take bayarwa a wannan fanni, zai taimaka wajen cimma nasarar manufofin ci gaba mai dorewa na SDGs.
Aikin na tsawon shekaru uku wanda kasar Sin ta gabatar ta kuma ba da taimakon kudaden da suka kai dala miliyan biyu, zai taimaka wajen kara samar da makamashin da ake iya sabuntawa ga al'ummomin Habasha da Sri Lanka, ta hanyar mayar da hankali wajen gwada amfani da gas da ake samarwa daga tsirrai da fasahohin karfin rana.
A nata jawabin, jami'ar tattalin arziki da harkokin cinikayya a ofishin jakadancin Sin dake Habasha, Liu Yu, ta nanata kudurin kasar Sin, na raba kwarewarta tare da hada kai da abokan hulda dake cikin hadin gwiwar kasashe masu tasowa, ta yadda za a kara raya makamashi mai dorewa.(Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China