2019-08-08 15:58:10 cri |
Zhang Xiaoming, ya yi wannan tsokaci ne yayin wani taron musayar ra'ayi da ofishin kula da harkokin yankunan Hong Kong da Macao na majalisar gudanarwar kasar Sin gami da ofishin gwamnatin tsakiyar kasar Sin dake Hong Kong suka shirya, yana mai cewa Hong Kong na fuskantar yanayi mafi tsanani a tarihinsa, tun bayan dawowarsa karkashin kasar Sin.
Sama da mutane 550 ne suka halarci taron na ranar Laraba, ciki hadda manyan jami'an majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da wakilan majalisar bada shawara kan harkokin yankin Hong Kong, da shugabannin kungiyoyin siyasa, da kungiyoyin al'umma masu kishin yankin. Kazalika akwai wakilai daga kungiyoyin masu ruwa da tsaki na matasa, da na sashen ilimi, da kungiyoyin kwararru, da kuma na kamfanonin babban yankin Sin masu hada hada a yankin na Hong Kong. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China