Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sinawa biliyan 1.4 ne suke tsaron tutar kasa mai taurari biyar
2019-08-05 19:16:41        cri

Jiya Lahadi da dare, mazauna tashar ruwa ta Victoria dake yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, sun kunna fitilu masu haske a gabobi biyu na tashar ruwan domin nuna aniyyarsu ta tabbtar da tsaron tutar kasar Sin mai taurari biyar, tare kuma da kiyaye mutuncin kasar ta Sin. Sun kuma rataya wasu kalamai a kan shahararrun gine-gine, inda suka rubuta jimloli kamar haka: "Yankin Hong Kong yana da makoma mai haske", da "Hong Kong ne gida na, ina kaunar Hong Kong, We Love Hong Kong ", kana aka kunna fitilun masu siffar tutar kasa mai launin ja da taurari biyar, fitilun da suka jawo hankalin jama'a matuka.

Bangarori daban daban da mazauna yankin Hong Kong sun kudiri niyyar tsaron yankin da tsarin "kasa daya amma tsarin mulki iri biyu' tare, ko shakka babu makomar Hong Kong tana da haske.

A kan dandalin sada zumunta kuwa, masu amfani da yanar gizo su ma sun nuna sha'awa matuka kan aikin tsaron tutar kasar Sin mai taurari biyar.

Labarin sashen gabatar da labarai na CCTV kan batun "Sinawa biliyan 1.4 suna tsaron tutar kasa mai taurari biyar tare" ya fi jawo hankalin masu amfanin manhajar Weibo, inda suka bayyana cewa, za su sauke nauyin dake wuyansu na tsaron tutar kasa, kawo yanzu adadin mutanen da suka karanta labarin ya kai biliyan 1 da miliyan 970, kana labarin ya samu masu yabo har sau miliyan 10, kana kusan mutane dubu 400 ne suka yi sharhin kan labarin

Hakazalika, wasu sun gabatar da labarai wadanda suke shafar tutar kasar Sin, hakika wadannan ba labarai ba ne, batu ne na kishin kasa dake burge jama'a matuka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China