Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci al'ummar Hong Kong su dakatar da tada rikici
2019-08-07 10:43:47        cri
Kakakin ofishin kula da harkokin yankunan Macao da Hong Kong a majalisar gudanarwar kasar Sin, Yang Guang, ya bukaci al'ummar Hong Kong da su daina tada rikici, su kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

Yang Guang wanda ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai jiya Talata, ya ce wannan hakki ne da ya rataya a wuyan dukkan mazauna yankin, la'akari da yanayin da ake ciki yanzu.

Ya ce suna fatan masu kishin yankin Hong Kong za su yi tunani a tsanaki, kan wanda zai wahala idan rikicin ya ta'azzara da kuma wanda zai ci riba.

Ya kuma jaddada cewa, dukkan sassa da hukumomin Hong Kong, ba za su taba lamuntar keta dokoki ba.

Da yake jaddada goyon bayan gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ga kantomar yankin Carrie Lam, ya ce yunkurin 'yan adawa na tilasta mata yin murabus ba zai yi tasiri ba.

A nasa bangaren, Xu Luying, shi ma kakakin ofishin kula da harkokin yankunan Macao da Hong Kong na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya ce wasu ne suka kitsa rikcin da ake yi a Hong Kong domin illata yankin.

Ya ce sun yi amfani da matasa domin cimma bukatunsu na siyasa, yana mai cewa karin matasa za su farga, su gane ainihin manufar mutanen, su kuma fahimci kuskuren da suka tafka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China