Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Haramcin da Amurka ta sakawa kasar Sin ya tsananta halin da manoman Amurka ke ciki
2019-05-27 20:16:08        cri
Jaridar New York Times ta Amurka ta wallafa wani sharhi dake cewa, haramcin da gwamnatin kasar Amurka ta sakawa kamfanin Huawei na kasar Sin ya dakatar da ayyukan gina ababen sadarwa a yankunan karkarar Amurka, inda masu filayen noma suka gaza tuntubar takwarorinsu dake sauran wurare. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta ji dadin mawuyacin halin da manoma da makiyayan Amurka suka shiga ba, amma a cewarta, ba laifin kasar Sin ba ne.

Lu ya ce, wasu jami'an gwamnatin Amurka na kokarin matsawa kamfanin Huawei lamba, ba tare da wasu kwararan shaidu ba, matakin da suka dauka na yin illa ga harkokin rayuwa gami da ayyukan jama'a da na masu sayayyar Amurka. A cewar Lu, ba abun mamaki ba ne a samu Amurkawa da suka nuna tababa ko kin yarda da abun da gwamnatinsu ta yi.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China