Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi gwaje-gwajen tashin jirgin sama samfuri GA20 kirar kasar Sin
2019-08-08 10:48:58        cri

Kamfanin kirar jiragen sama na Guanyi dake lardin Jiangxi na kasar Sin, ya ba da labari a jiya Laraba cewa, jirgin sama samfuri GA20 da kamfanin ya kera bisa fasahar kansa, an yi gwaje-gwajen tuka shi a sararin samaniya har tsawon mita 3000, a karo na farko kuma an samu nasarar gwajin.

Jirgin saman samfuri GA20, ya kasance jirgin na farko da kamfani mai zaman kansa na kasar Sin ya kera, an kuma fara aikin ne tun daga shekarar 2015. An kwashe shekaru 3 an gudanar da tsare-tsare da gwaje-gwaje. Wannan jirgi dai na da amfani a fannoni daban-daban, ciki hadda ba da horaswa a fannin tashin jirgin sama, da yawon shakatawa da dai sauransu.

An ce, wannan ne karo na 50 da ake gwajin tashi wannan jirgi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China