Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kudaden da mazauna karkara ke iya samu bayan haraji a sassan kasar Sin sun ninka sau 40 cikin shekaru 70
2019-08-08 10:35:50        cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ko NBS a takaice, ta ce kudaden shiga, da na kashewa da Sinawa mazauna karkara ke samu, sun yi matukar karuwa cikin shekaru 70 da suka gabata.

Hukumar ta fitar da wasu alkaluma dake nuna cewa, a shekarar 2018, adadin yawan kudaden da mazauna yankunan karkarar kasar Sin ke samu bayan cire haraji, sun ninka na shekarar 1949 da kusan rubi 40, inda adadin ya kai kudin kasar yuan 14,617, kwatankwacin dalar Amurka 2,088 ga ko wane mutum, idan an kauda batun sauyin farashin kayayyaki, wanda kuma bisa matsakaicin kiyasi, adadin ke karuwa da kaso 5.5 bisa dari a duk shekara.

Har wa yau hukumar ta NBS ta ce, gibin kudaden shiga bayan cire haraji na mazauna birane, idan an kwatanta da na mazauna karkara ya yi matukar raguwa, inda gibin wannan adadi ya tsaya a kaso 2.69 a shekarar 2018, wato dai adadin ya ragu da kaso 0.64 bisa dari, idan an kwatanta da na shekarar 1956.

A daya hannun kuma, adadin yawan kudi da mazauna kauyukan kasar ta Sin ke kashewa cikin shekarun 70 ya karu, wanda hakan ke nuni ga fadadar wadata da karkon tattalin arzikinsu.

Har ila yau, fadin muhallan al'umma mazauna karkara bisa kiyasi, ya kai sakwaya kilomita 47.3, wanda ya haura sakwaya kilomita 8.1 da suke iya samu a shekarar 1978.

Gane da batun sayayya kuwa, a shekarar 2018, mazauna karkara sun samu damar mallakar karin ababen more rayuwa, inda bisa kiyasi, cikin ko wane gida a jimillar iyalai 100, adadin masu mallakar motoci ya kai kaso 22.3 bisa dari, na masu mallakar kwanfutoci kuma ya kai kaso 26.9 bisa dari, sai kuma masu mallakar wayoyin salula da ya kai kaso 257. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China