Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kaiwa Alkahira
2019-08-07 10:51:50        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta zanta da manema labarai a jiya Talata inda ta ce Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kaiwa birnin Alkahira fadar mulkin Masar, kuma ta nuna alhini sosai ga wadanda suka rasa rayukansu cikin harin, da kuma jajantawa wadanda suka ji rauni da iyalan mamatan.

An ba da labarin cewa, an kai hari birnin Alkahira ne da safiyar ranar 5 ga wata, lamarin da ya hallaka mutane 20 yayin da wasu 48 suka ji rauni.

Hua Chunying ta ce, Sin na adawa da ko wane irin ta'addanci, kuma tana nacewa ga goyon bayan kokarin da Masar take yi wajen tabbatar da zaman lafiya mai karko a kasar da dakile ta'addanci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China