Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta nuna adawa da janyewar Amurka daga yarjejeniyar INF
2019-08-07 09:31:57        cri
Jakadan Sin game da kwance damarar makamai Li Song, ya ce kasar sa ta yi takaici, tare da nuna adawar ta da janyewar Amurka daga yarjejeniyar da aka cimma, kan matsakaitan makaman nukiliya ko INF a takaice, ba tare da la'akari da matsayar sauran kasashen duniya game da hakan ba.

Li Song, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin taron kwance damarar makamai da ya gudana. Ya ce tun bayan da Amurka ta bayyana wannan mataki na ta a hukumance a ranar 2 ga watan nan na Agusta, wasu manyan jami'an gwamnatin kasar ke bayyana shirin Amurkan, na sake komawa ayyukan samarwa, da kuma girke matsakaitan makaman nukiliya.

Jami'in ya ce ko shakka babu, wannan mataki ya nuna yadda Amurka ke daukar matakai na kashin kai da basu dace ba, wadanda kuma suka sabawa alkawuran ta game da cudanyar kasa da kasa.

Yayin da take ayyana ficewa daga yarjejeniyar ta INF, Amurka ta ce an kawo karshen yarjejeniyar dake tsakanin ta da Rasha game da kwance damarar makaman nukiliya, kuma tana neman ganin shigar Sin tattauna, game da batun makaman nukiliya tsakanin ta da Amurka da kuma Rasha. Game da batun, jami'in kasar Sin ya ce "Amurka ta yi ikirarin don karkatar da hankalin al'ummun duniya kawai. Sin kuwa ba ta da niyyar shiga a dama da ita a wannan lamari".

Kaza lika jakadan na Sin ya jaddada matsayar kasar sa don gane da makaman nukiliya, cewa za ta nacewa tsarin kariyar kai a fayyace, kuma a kayyade. Kana Sin ba za ta taba amfani da su wajen yin barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China