Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta amsa tambaya game da matakin gwamnatin Indiya na kafa yankin Ladakh
2019-08-06 20:13:42        cri

Yau Talata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta amsa tambaya game da kafa yankin tsakiya na Ladakh da gwamnatin kasar Indiya ta yi, matakin dake da alaka da yankin kasar Sin.

Hua Chunying ta ce, Sin tana adawa da matakin Indiya na mayar da yankin dake kan iyakar kasashen biyu, wanda yake karkashin ikon kasar Sin zuwa karkashin ikonta. A kwanakin nan, Indiya ta keta 'yancin kasar Sin ta hanyar yiwa dokarta gyaran fuska, matakin da kasar Sin ba za ta yarda ba, kuma ba zai yi wani tasiri ba.

Sin ta bukaci bangaren Indiya, da ya yi taka-tsantsan game da batun kan iyakar kasashen biyu, ya kuma martaba yarjeniyoyin da bangarorin biyu suka cimma, ta kuma guji daukar matakan da za su kara dagula batun kan iyakarsu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China