Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alibaba da Tencent na kasar Sin sun shiga cikin manyan kamfanoni 10 mafi daraja a duniya
2019-06-12 10:12:31        cri

Kamfanin kasuwanci ta intanet na Alibaba da kamfanin fasaha na Tencent, sun shiga cikin kamfanoni 10 mafi daraja a duniya.

Wani rahoto da kamfanin samar da hidimar sadarwa ta waya ta WPP da cibiyar tuntuba kan inganta kamfanoni ta Kantar Millward Brown suka fitar a jiya, ya ce darajar kamfanin Alibaba ya karu da kaso 16 zuwa dala biliyan 131.2 akan na bara, inda ya haye matakai 2 zuwa mataki na 7, har ya zarce kamfanin Tencent a karon farko, don zama kamfanin kasar Sin mafi daraja.

Tencet wanda ke da mazauni a birnin Shenzhen na kasar Sin, da aka fi sani saboda manhajarsa ta waya wato Wechat, shi ne a matakin na 8 a jerin kamfanonin, inda ya sauka da matakai 3 idan aka kwatanta da bara, bayan darajarsa ya sauka da kaso 27 zuwa dala biliyan 130.9.

David Roth, shugaban ofishin WPP a yankin Asia, kuma shugaban kamfanin BrandZ, ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, darajar kamfanonin kasar Sin na saurin karuwa, la'akari da kamfanonin kasar 16 da suka shiga jerin manyan kamfanonin 100 na duniya, idan aka kwatanta da guda daya da ya shiga a shekarar 2016. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China