Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangaren raya al'adu bisa fasahar zamani na kasar Sin zai samu ci gaba mai karfi a zamanin amfani da fasahar 5G
2019-08-05 15:00:31        cri

Bangaren raya al'adu bisa fasahar zamani na kasar Sin na sa ran samun gagarumin ci gaba yayin da sabbin fasahohi ke zama hanyoyi masu karfi na samarwa da inganta kayayyaki da hidimomi a bangaren.

A cewar rahoton yanayin masana'antar raya al'adu bisa fasahar zamani da cibiyar raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin da cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar da cibiyar bincike ta Tencent suka fitar a karshen mako, ana sa ran amfani da fasahar sadarwa ta 5G da runbun adana manyan bayanai da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam da sauran fasahohin zamani, za su samar da sauye-sauye masu muhimmanci ga bangaren.

Alkaluman hukumar kididdiga ta kasar Sin sun nuna cewa, bangaren yana ta habaka a shekarun baya-bayan nan ba tare da tangarda ba. Jimilar kudin shigar da bangaren da harkokin kasuwanci masu alaka da shi suka samu ya kai yuan triliyan 4.06, kwatankwacin dala biliyan 588 a rabin farko na bana, adadin da ya karu da kaso 7.9. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China