Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kara rage wa kamfanoni kudaden da suke biya
2019-07-25 10:10:35        cri

Majalisar gudanarwar kasar Sin, ta yanke shawarar kara rage matsin biyan kudade ga kamfanoni da nufin kara bunkasa harkokin kasuwanci.

Sanarwar da aka fitar bayan taron majalisar na jiya, wanda Firaministan kasar Li Keqiang ya jagoranta, ta ce za a kara kokarin kawar da kudaden da ake cajin kamfanoni ba bisa ka'ida ba, domin tabbatar da ingancin manufofin rage haraji da kudaden da suke biya.

A cewar sanarwar, an haramta wa sassan gwamnatin mayar da kudaden da suka kashe kan kamfanonin, sannan bai kamata kungiyoyin 'yan kasuwa ko cibiyoyin gwamnati su yi amfani da ikonsu wajen neman a biya su kudi ba bisa ka'ida ba.

Ta ce dole ne a bayyana dukkan wasu kudade da ya kamata kamfanoni su biya, bisa tabbatar da adalci da kuma sa ido.

Taron ya kuma yanke shawarar matse kaimi kan yin garambawul ga tsarin hada hadar kudi domin inganta rawar da hada-hadar kudi ke takawa wajen goyon bayan yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare da ci gaban tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China