2019-07-29 19:42:27 cri |
Yang Guang, ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, biyowa bayan zanga zanga da yamutsi, da suka auku a yankin musamman na Hong Kong, yayin da yake tsokaci gaban taron 'yan jaridu da ya gudana a nan birnin Beijing.
Jami'in ya ce, 'yan sandan Hong Kong sun amince, tare da ba da kariya ga masu zanga zanga cikin lumana bisa doka, sakamakon rashin amincewar da ta biyo bayan dokar mika masu manyan laifuka babban yankin Sin domin fuskantar hukunci, da ma batutuwa masu nasaba da samun tallafin shari'ar da ta shafi hakan.
To sai dai kuma, Yang ya ce karya dokoki da wasu tsageru suka rika yi tun daga ranar 12 ga watan Yuni, ya zarta batun zanga zanga. Ya ce tarzoma da yamutsin a yankin Hong Kong sun haura wata daya, lamarin da ya haifar da karya doka da oda, da gurgunta yanayin zamantakewa, da tattalin arziki, da ma kwanciyar hankalin al'ummar yankin. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China