Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi fatan ganin Amurka ta rungumi akidar daina tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong
2019-07-31 20:17:59        cri
A kwanakin baya ne ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta musanta ikirarin dake nuna cewa, akwai wasu kasashen waje dake rura wutar rikici a Hong Kong a halin yanzu. Game da hakan, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta ce, Sin na fatan ganin cewa Amurka, ta iya gabatar da shaidu, ko alkawarta cewa ba za ta yi shisshigi cikin harkokin yankin Hong Kong ta duk wata hanya ba.

Hua ta ce, tana da yakinin cewa daukacin al'ummar kasar Sin, ciki har da mazauna yankin Hong Kong sama da miliyan bakwai, suna matukar fatan ganin yankin Hong Kong ya ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, gami da bunkasuwa. Ta kuma yi kira ga kafofin watsa labarai, da su tsaya kan gaskiya, da rike amana, lokacin da suke bayar da rahotanni game da harkokin da suka shafi Hong Kong. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China