Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi kira a yunkura wajen magance yaduwar Ebola a DRC
2019-07-20 16:11:36        cri

Tarayyar Afrika AU ta yi kira ga kasa da kasa, su gaggauta daukar mataki kan cutar Ebola da ta ki-ci-ta-ki cinyewa kusan shekara 1, tare da sanadin mutuwar mutane da dama a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo DRC.

Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai a hedkwatar AU dake Addis Ababa na Habasha, John Nkengasong, daraktan cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta Afrika, ya ce ya zuwa ranar 17 ga watan nan na Yuli, mutane 2,438 ne aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma 1,621 da suka mutu sanadiyyarta a kasar.

Jami'in ya kuma jaddadawa wadanda suka kamu da ita cewa, kamuwa da cutar ba ta nufin mutuwa.

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, kula da cutar a matakinta na farko zai iya inganta damar mutum na rayuwa.

La'akari da sabbin matakan tunkarar cutar, John Nkengasong, ya ce AU za ta kara tura karin jami'an agaji kasar, yana mai cewa, cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta Afrika za ta hada hannu da kwamitin sulhu na AU da tsarin tsaro na MDD wajen tabbatar da tsaro a fannin kiwon lafiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China