Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan hatsin da kasar Sin ta samar ya kusan rubanyawa sau 5 cikin shekaru 70 da suka gabata
2019-08-06 09:41:50        cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ce bangaren aikin gona na kasar, ya samu ci gaba cikin sauri cikin shekaru 70 da suka gabata, inda yawan hatsin da ta samu ya rubanya har sau 4.8.

A cewar rahoton da hukumar ta fitar, yawan hatsin da kasar Sin take samu kan matsakaicin matakin kaso 2.6 daga shekarar 1949, ya karu zuwa kilogram biliyan 658 a shekarar 2018, adadin dake iya ciyar da kaso 20 na al'ummar duniya, da aka samu daga kasa da kaso 9 na jimilar kasar noma a duniya.

Kasar ta kara baza komarta a bangaren samar da abinci ta hanyar samar da hanyoyin inganta iri da dabbobi, inda kayayyakin ruwa da take samarwa ke kan gaba a duniya tun daga shekarar 1989, wanda ya tsaya a kan ton miliyan 64.6 a shekarar 2018, adadin da ya dara na shekarar 1949 har sau 143.

Yanayin bangaren aikin gona na ci gaba da ingantuwa, la'akari da rungumar tsarin zamani dake inganta ci gaba ta kowacce fuska a bangaren aikin noma da raya dazuka da kiwo da kiwon kifi, wadanda suka maye gurbin tsarin noma na gargajiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China