Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An inganta wuraren cajin motoci masu amfani da makamashi mai tsafta a Tianjin
2019-08-06 13:57:59        cri

Hukumomi a Tianjin sun inganta tsarin caji domin biyan bukatun motoci masu amfani da makamashi mai tsafta a birnin.

Kamfanin samar da lantarki na Tianjin, ya ce kawo yanzu, an gina tashoshin caji masu matukar sauri guda 43, wadanda kuma ke da ramukan caji 191

Kamfanin ya ce an kafa ramukan caji a dukkan manyan tituna 13 da suka ratsa Tianjin, wadanda za su ba direbobi daga Beijing da Tianjin da lardin Hebei damar yin caji idan suna bukata.

Alkaluma sun nuna cewa, a bana, karfin wutar lantarki a tashoshin caji masu matukar sauri ya kai kwh 2,300, adadin da ya karu kan na bara da kaso 201.44.

Saboda manufofin gwamnatin, bangaren motoci masu amfani da makamashi mai tsafta ya samu ci gaba sosai, inda aka sayar da motocin da yawansu ya kai sama da miliyan 1.26 ya zuwa karshen shekarar 2018, adadin da ya zarce abun da ya gaza 10,000 a shekarar 2009. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China