Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarori daban-daban na Hongkong sun yi zaman taro mai taken "Kiyaye Hongkong"
2019-07-21 16:29:04        cri

Jiya Asaba da yamma, jama'ar Hongkong fiye da dubu 300 sun yi zaman taro mai taken "Kiyaye Hongkong" cikin ruwan sama, don nuna rashin jin dadi kan nuna karfin tuwo, da goyon bayan 'yan sanda don neman su kiyaye zaman doka da oda da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Jama'ar sun kuma nuna mutuntawa da girmamawa ga 'yan sanda a yankin. Wani masanin dokoki Lawrence Ma, ya nuna cewa, ya kamata a kare 'yan sanda saboda sun sadaukar da kansu don tabbatar da zaman lafiya a yankin. Madam Liu, ma'aikaciyar hada-hadar gidaje, ta ce, jama'ar Hongkong na kokarin kiyaye zaman lafiyar yankin, masu tsattsauran ra'ayi ba za su iya wakiltar mazauna yankin Hongkong ba. Zheng Zhenxi, dalibin da ya kammala karatu a jami'ar Hongkong a bana ya ba da jawabi cewa, duk da cewa matasa da al'umma na fuskantar wasu matsaloli, amma ba za a iya tinkarar su ta hanyar nuna karfin tuwo da daukar matakai masu sabawa doka ba. Yau suna taro don kwantar da hankali a yankin.

An ba da labari cewa, a yayin taron, kungiyoyin kasuwanci mafiya girma biyar sun yi kira ga al'ummar yankin da su yi kokarin farfado da yanayi mai kyau ta fuskar ciniki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China