Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadu daga kasashe 50 sun bayyana goyon bayansu ga matsayar kasar Sin kan batun jihar Xinjiang
2019-07-27 16:03:36        cri
Jakadun kasashe 50 dake ofishin MDD na Geneva, sun rattaba hannu kan wata wasika da suka aikewa shugaban hukumar kare hakkin dan Adam da babbar kwamishinar dake kula da hakkokin dan Adam ta majalisar, inda suka bayyana goyon bayansu ga matsayar kasar Sin dangane da batun jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar.

Tawagar kasar Sin a Geneva, ta ce tun da farko a ranar 12 ga watan nan, wasu jakadun ofishin na Geneva, sun aike da wasika domin nuna goyon bayansu ga Kasar Sin, kuma ya zuwa yammacin jiya Juma'a, wasu karin Jakadu sun bi sahunsu wajen nuna goyon bayansu ga Kasar Sin.

Cikin wata sanarwa da aka fitar jiya da daddare, tawagar ta Kasar Sin, ta ce wasu kasashe sun kuma bayyana goyon bayansu a wasiku ko taron manema labarai daban daban.

A wasikar ta hadin gwiwa, jakadun sun yabawa Kasar Sin bisa nasarorinta a fannin tattalin arziki da zaman takewa da ingantacciyar hanyar yaki da ta'addanci da matakan kawar da tsattsauran ra'ayi da kuma tabbatar da hakkin dan Adam.

Sun kuma yaba da damarmakin da Kasar Sin ta bayar ga jakadun kasashen waje da jami'an hukumomin kasa da kasa da 'yan jarida na ziyartar jihar Xinxiang, domin bayyana bambancin dake tsakanin abun da masu ziyarar suka ganewa idonsu da kuma wanda kafafen yada labaran yammacin duniya ke fada.

Jakadun sun kuma bukaci wasu rukunin kasashe, su dakatar da amfani da bayanai marasa sahihanci wajen ayyana zargi mara tushe akan kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China