![]() |
|
2019-07-30 10:13:11 cri |
Wu ya ce, ya kamata al'ummar Libya su tsara makomar kasarsu, a hannu guda kuma al'ummomin kasa da kasa su mutunta 'yanci da cikakkun yankunan kasar.
Jami'in na kasar Sin ya kuma yi kira da a yi amfani da matakai na siyasa, wajen daidaita rikicin da kasar ke fama da shi a halin yanzu. Yana mai cewa, ya kamata dukkan bangarorin kasar da abin ya shafa, su himmatu wajen cimma matsalar siyasa da kuma wajibi ne a warware batun kasar ta Libya ta hanyar siyasa.
Kafin kalaman na WU, sai da wakilin musamman na babban sakataren MDD a Libya Ghassan Salame, ya ba da rahoton cewa, tun lokacin da fada ya barke a kewayen birnin Tripoli a farkon watan Afrilun wannan shekara zuwa wannan lokaci, mutane 1,100 ne suke rasa rayukansu, ciki har da fararen hula 106.
Salame ya ba da shawarar daukar matakai uku, don kawo karshen rikicin kasar. Na farko shi ne, ayyana doka kan Eid al-Adha, bikin sallar Lahiya, da shirya tattaunawar manyan jami'an kasashen da abin ya shafa, don kawo karshen tashin hankalin kasar, a aiwatar da takunkumin hana sayar da makamai da kwamitin sulhu ya kakabawa kasar, sannan a shirya ganawar masu ruwa da tsaki daga Libya domin su amince a kai ga samun nasarar da ake fata. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China