Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Yara miliyan 20 ne ba su samu alluran rigakafin cututtaka dake kisa ba a shekarar 2018
2019-07-16 14:11:25        cri
Wani rahoton hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya (WHO) da asusun tallafawa yara na MDD (UNICEF) suka wallafa a jiya, ya nuna cewa, kusan yara miliyan 20 a duniya ne, ba a yiwa allurar rigakafin cututtukan dake hallaka yara a shekarar 2018 da ta gabata ba.

Rahoton hukumomin biyu ya nuna cewa, sama da yaro guda cikin 10 ne ba a yiwa rigakafin cututtukan da suka hada da zawo da tetanus da tarin fuka da kyanda ba, adadin da ya kai kaso 86 cikin 100 tun a shekarar 2010.

Alkaluma na nuna cewa, yankin da ya fi mayar da hankali wajen yiwa yara rigakafi a shekarar 2018 shi ne yankin Turai, inda adadin yaran yankin da aka yiwa rigakafin ya kai sama da kaso 90 cikin 100, sama da kaso 18 cikin 100 kan na nahiyar Afirka, yankin da ke da adadi mafi karanta.

Rahoton ya kara da cewa, galibin yaran dake zaune a kasashe mafiya fama da talauci a duniya, da kasashen masu hadari ko wadanda tashin hankali ya shafa, su ne ba sa samun irin wadannan rigakafi.

Kusan rabi daga cikin yaran dake fuskantar wannan hadari, suna zaune ne a kasashe 16 da suka hada da Afghanistan, da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, da Chadi,da Jamhuriyar demokiradiyar Congo(DRC) da Habasha. Sauran sun hada da Haiti, da Iraki da Mali da Nijar, da Najeriya. Sai kuma kasashen Pakistan da Somaliya, da Sudan ta kudu da Sudan da Syria da kuma Yemen.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China