Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Sama da mutane miliyan 820 ne suka yi fama da talauci a 2018
2019-07-16 13:59:13        cri

Wani rahoton MDD ya ce adadin masu fama da yunwa a duniya na ci gaba da karuwa, inda mutane sama da miliyan 820 da suka yi fama da ita a shekarar 2018.

Rahoton mai taken "Yanayin wadatuwar abinci da sinadaran gina jiki a duniya a shekarar 2019" da aka kaddamar a hedkwatar MDD dake New York, ya ce bayan gomman shekaru da tabarbarewar yanayin wadatuwar abinci, yanayin yunwa la'akari da yawan tamowa, ya sauya a shekarar 2015.

Yayin da adadin bai sauya ba cikin shekaru 3 da suka gabata kan kasa da kaso 11 bisa dari, adadin wadanda suke fama da yunwa ya karu a hankali inda ya kai miliyan 821.6 a shekarar 2018.

Hukumar samar da abinci da kula da aikin gona ta MDD FAO da asusun kula da yara na MDD UNICEF da hukumar lafiya ta duniya da kuma asusun kasa da kasa na raya aikin gona da kuma shirin samar da abinci na duniya ne suka hada rahoton. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China