Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta kara yin kira da a dauki matakan dakile aurar da yara kanana
2019-07-12 10:53:04        cri

Jami'ar tsare tsare ta ayyukan MDD a kasar Zambia Coumba Gadio, ta yi kira ga kasashen duniya, da su sabunta kwazon su wajen dakile matsalar aurar da yara kanana.

Coumba Gadio, ta ce auren wuri ga yara kanana na kunshe da keta hakkokin yara, yana kuma ba da damar keta hurumin 'yan mata masu kananan shekaru, baya ga hadarin kamuwa da cututtukan jima'i, ciki hadda HIV ko Sida tsakanin yara masu karancin shekaru.

Jami'ar ta bayyana hakan ne, yayin taron kwamitin tawagogin kasashe da na kungiyoyi daga kwamitin gudanarwar asusun MDD mai kula da yawan al'umma ko UNFPA a takaice, da takwarorin su na asusun kananan yara na MDD UNICEF, da shirin kasa da kasa game da gaggauta matakan kawo karshen auren wuri ga yara.

Kwamitin dai ya yi tarukan sa na masu ruwa da tsaki a wannan karo a kasar Zambia ne, da nufin zakulo hanyoyin dakile kalubalen aurar da yara masu karancin shekaru a sassan duniya. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China