Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ci gaban kasar Sin zai haifarwa nahiyar Afirka damammaki, in ji jami'in UNCTAD
2019-07-10 11:12:53        cri
Darakta a sashen tsara samar da ci gaba, a taron karawa juna sani na MDD game da cinikayya da bunkasuwa Richard Kozul-Wright, ya ce cikin shekaru 20 da suka gabata, kasar Sin na bin wani tafarkin ci gaba mai dorewa, wanda ko shakka babu zai haifarwa kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka da wasu damammaki na bunkasuwa.

Richard Kozul-Wright, ya yi wannan tsokaci ne, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yana mai cewa hadin gwiwa tsakanin Sin da nahiyar Afirka, na haifar da nasara a fannin ci gaba mai dorewa, da kuma kyautata zamantakewar al'umma. Kaza lika wannan alaka na samar da damammaki, wadanda bayan batun albarkatu, tana kuma ba da damar koyo da musayar kwarewa.

Daga nan sai ya jaddada muhimmancin musaya, da cin gajiyar da kasashe masu tasowa ciki hadda Afirka ke yi daga kwarewar Sin a fannin samar da ci gaba. Ya ce wannan kawance shi ne mafi alfanu, sama da wanda ke wanzuwa tsakanin masu ba da taimako da masu karba. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China