Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNAIDS:Ba za a cimma burin dakile cutar Kanjamau na shekarar 2020 ba
2019-07-18 14:18:25        cri

Hukumar kula da aikin dakile cutar Kanjamau ta MDD UNAIDS ta gabatar da wani rahoto a kasar Afirka ta Kudu a ranar Talata da ta gabata cewa, mutane kimanin dubu 770 ne suka mutu a bara sakamakon cutar Kanjamau a duniya, saboda haka hukumar ta yi hasashen cewa, ba za a cimma burin da aka sanya na rage wadanda suke rasa rayuka sakamakon cutar zuwa kasa da dubu 500 a shekarar 2020 ba.

A cewar hukumar UNAIDS, aikin da ake yi, na rage wadanda ke kamuwa da cutar Kanjamau, da jinyar karin mutane masu kamuwa da cutar, gami da rage yawan mutanen da suke rasa rayuka sakamakon cutar, na fuskantar wani yanayi na tafiyar hawainiya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China