Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Amurka ce ke kawo cikas ga hadin gwiwar kasa da kasa a kokarin neman ci gaba
2019-07-26 20:14:00        cri

A kwanakin baya ne, wasu Amurkawa fiye da 100 dake kin jinin kasar Sin suka mikawa shugaban kasar Amurka Donald Trump wata wasikar hadin gwiwa a fili, inda suka zargi kasar Sin da amfani da moriyar tattalin arziki wajen jawo hankalin kawayen Amurka da sauran kasashen duniya, ta yadda za ta yayata tasirinta a duk fadin duniya. A zahiri, wannan ra'ayi yana lalata kokarin da kasar Sin ke yi kan yadda sauran kasashen duniya za su iya cin gajiyar bunkasar tattalin arzikin kasar Sin.

A hakika dai, matakan kashin kai da na ba da kariya ga cinikayya na wasu 'yan siyasar Amurka ne ke kawo cikas ga kokarin neman ci gaba ta hanyar yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa.

A 'yan shekarun baya, kasar Amurka ta dauki matakan kara haraji kan kayayyakin kasar Sin, da kuma kafa ginshikan cinikayya a ko'ina, har ma ta kuntatawa sassa daban daban dake samar da kayayyaki a duk fadin duniya, kuma ta kawo barazana matuka ga harkokin cinikayya da zuba jari da tattalin arziki na duniya da ake yi, domin biyan bukatunta kawai.

Wani rahoto da bankin duniya ya fitar a watan Yunin, ya yi hasashen cewa, yawan kudin cinikayyar da ake yi tsakanin kasa da kasa a shekarar 2019 zai karu da 2.6% ne kawai, wato zai kai matsayi mafi kankanta bayan aukuwar rikicin hada-hadar kudi a shekarar 2008.

Ban da haka, yadda kasar Amurka take yin babakere a fannin kimiyya da fasaha yana haifar da babbar matsala ga yunkurin bil Adama na neman samun cigaban kimiyya da fasaha, gami da al'adu. Misali, a kokarin ganin ta koma matsayi na farko a fannin wasu sabbin fasahohi, kamar fasahar sadarwa ta 5G, kasar Amurka ta yi amfani da tasirinta a fannin siyasa wajen kokarin haifar da matsala ga kamfanonin kasar Sin, har ma ta sa wasu kamfanoninta su daina samar da kayayyaki ga takwarorinsu na kasar Sin. Ma iya cewa, yadda kasar Amurka take kokarin hana ruwa gudu ga ci gaban kimiyya da fasaha a duniya, ya nuna rashin kunyarta, da wata mummunar aniyyar da take da ita.

Sakamakon akidarta ta yin babakere da son kai, kasar Amurka tana kara gurgunta kokarin kasashen duniya na neman ci gaba. Duk da haka, wasu 'yan siyasan kasar sun yi biris da wannan batu, sa'an nan sun fara yada jita-jita game da kasar Sin, inda suka ce wai kasar Sin na yin amfani da moriya a fannin tattalin arziki wajen dauke hankalin sauran kasashe, don neman yin tasiri a kansu. Wannan zance mai kama da wasan yara, abin dariya ne. Domin kowa ya san kasar Sin babbar kasa ce dake kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta. Sin tana kokarin raya kanta, don neman biyan bukatun jama'arta na neman kyautata zaman rayuwarsu, haka kuma tana neman ta taimaki sauran kasashe da al'ummunsu.

A cikin shekaru da yawa da suka wuce, kasar Sin ta dade tana samar da gudunmawar da ta kai kashi 30% ga karuwar tattalin arzikin duniya, alkaluma mafi yawa a duniya. Sa'an nan manyan kasuwannin dake cikin kasar Sin na samar da dimbin riba ga kamfanonin kasa da kasa. Yayin da cikakkun tsare-tsaren kasar Sin a fannin masana'antu sun baiwa kasashen duniyar damar kyautata dabarunsu na raba kayayyaki, da samar da karin kayan masana'antu. Ban da wannan kuma, butakun cikin gidan kasar Sin, da jarin da take zubawa, sun samar da dimbin guraben ayyukan yi a kasashe daban daban.

Sanin kowa ne cewa, Sin ce ta gabatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya" a shekarar 2013, a cikin wadannan shekaru 6 da suka gabata, yawan kudin ciniki tsakanin Sin da kasashen da cikin wannan shawarar ya kai fiye da dala triliyan 6, kuma yawan kudin da aka zuba a fannin da bai shafi hada-hadar kudi ba ya kai fiye da dala biliyan 90, kana yawan dandalin hadin kai da Sin ta kafa a kasashen ketare da shawarar ta shafa ya kai 82, matakin da ya sa yawan harajin da Sin take biya a wadannan kasashe ya kai fiye da dala biliyan 2, kana yawan guraben ayyukan yi da aka samar dangane da hakan ya kai dubu 300.

A halin yanzu, samun bunkasuwa shi ne abu mafi muhimmanci wajen warware rikici da matsaloli da Bil Adama ke fuskanta. A matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya, kamata ya yi Amurka ta ba da gudunmawa wajen rage gibin bunkasuwa tsakanin kasa da kasa a maimakon kawo cikas ga bunkasuwar sauran kasashe. (Sanusi, Bello, Amina)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China