Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na da "cikakkiyar azama" a fannin kara bude kofarta ga ketare
2019-07-02 21:15:57        cri

A yayin taron kolin G20 da aka yi a birnin Osakar Japan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanar da muhimman matakai 5, na hanzarta kara bude kofar kasar Sin ga ketare, sannan a yayin taron tattaunawa na lokacin zafi na Davos karo na 13 da ake yi a birnin Dalian na kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta sake bayyana niyyarta ta kara bude kofarta ga ketare, inda firaministan kasar Sin ya shelanta cewa, kasar Sin za ta bude kofar masana'antun samar da kayayyaki, da sana'o'in ba da hidimomi a fannin hada-hadar kudi, sannan za ta kara rage yawan harajin kwastam, da kara karfin kare 'yancin mallakar fasaha.

Bugu da kari, za ta kara bude kofofin wasu masana'antu a fili ga baki 'yan kasuwa da jarin waje. An dauki wadannan matakai dalla dalla ne, domin tabbatar da cika alkawarin kara bude kofar kasar Sin da shugaba Xi Jinping ya yi, a taron koli na G20 na Osaka, sun kuma bayyana cewa, kasar Sin wadda take hanzarta cika alkawuranta kamar yadda ya kamata, tana da "cikakkiyar azama".

Kwanaki 2 kawai bayan rufe taron kolin G20 a Osakan, kasar Sin ta cika sabon alkawarinta, na kara bude kofarta ga ketare ba tare da bata lokaci ba. A ranar 30 ga watan Yuni ne kasar Sin ta kaddamar da matakan musamman, game da bai wa masu jarin waje izinin zuba jari a kasar, sa'an nan karo na farko ta fitar da jerin sunayen sana'o'in da aka karfafa gwiwar masu jarin waje su zuba jari a cikin su, a kokarin mara wa masu jarin waje baya wajen kara zuba jari a fannin kera kayayyaki. Takaita jerin sana'o'i da ayyukan da aka haramta zuba jarin waje cikin su, da kuma fitar da jerin sana'o'i, da ayyukan da aka karfafa gwiwar zuba jarin waje kansu, sun shaida karfin kasar Sin na cika alkawarinta, na kara bude kofa ga ketare nan take ba tare da bata lokaci ba.

Kara bude kofa ga ketare, yana bukatar a rika himmantuwa a kai. Yanzu kasar Sin ta fara bude kofarta ga ketare ta fuskar tsare-tsare, ciki hadda kyautata dokoki da tsare-tsare masu nasaba da hakan. Sakamakon tsayawa kan ci gaba da bude kofarta ga ketare, ya sa kasar Sin ta samu amincewar masu jarin waje da kuma sha'awarsu, tare da kara wa kanta kuzarin raya kasa, yayin da ake fuskantar rashin tabbaci a duniya.

Alkaluman da aka samu daga taron MDD game da ciniki da aikin neman ci gaba wato UNCTD, sun nuna cewa, yawan jarin da aka zuba wa kasashen waje kai tsaye a bara ya ragu da kashi 13%, yayin da a nata bangare, kasuwar kasar Sin ta janyo karin jari daga ketare, wanda ya karu da kashi 4%. Sa'an nan a cikin farkon watanni 5 na bana, kasar Sin na samun karin jarin da ake zuba mata daga kasashen waje, inda take amfani da kudin da aka zuba mata da yawansa ya kai kudin RMB yuan biliyan 369 da wani abu, adadin da ya karu da kashi 6.8% bisa makamancin lokacin bara, sa'an nan saurin karuwar kudin ya ninka har fiye da sau 5. Wannan karuwa ta shaida karfin kasuwannin kasar Sin ta fuskar neman samun jarin waje.

A lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel, yayin taron kolin kungiyar G20 da ya gudana a Osaka na kasar Japan, shugaba Xi ya ce, "Alkawarin da kasar Sin ta yi na kara bude kofarta ga kasashen waje, za ta cika shi." Hakan na nufin, duk wata canzawar yanayi da ake fuskanta a duniya, kasar Sin za ta tsaya kan manufofinta na kara bude kofa ga kasashen waje, gami da neman tabbatar da moriyar juna yayin da take hadin kai da sauran kasashe. Kasar za ta kara kokarin kyautata muhallin cikin gidanta a fannonin kasuwanci da ciniki, sa'an nan za ta samar da karin damammakin samun riba ga masu zuba jari na kasashen waje, don kara samar da wani yanayi na tabbas ga duniyarmu. (Sanusi, Tassallah, Bello)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China