Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wadanda suka tsoma baki kan harkokin Hongkong da na cikin gidan kasar Sin ba za su ci nasara ko kadan ba
2019-07-02 20:47:39        cri

 

A jiya 1 ga watan Yuli, wato ranar cika shekaru 22 da dawowar yankin Hongkong cikin kasar Sin, wasu masu tsattsaurar ra'ayi sun kutsa kai cikin babban ginin majalisar kafa dokokin Hongkong, har ma sun karya doka sun lalata kayayyakin ginin kamar yadda suke so.

Yawancin kasashen duniya sun zirgi irin wannan mataki na nuna karfin tuwo mai tsanani da yake karya dokokin yankin Hongkong, kuma yake lalata halin zaman lafiya da ake ciki a yankin. Amma abin mamaki shi ne, kasashen Amurka da Ingila da kungiyar EU, sun ce ya kamata a tabbatar da "'yancin kai kara cikin ruwan sanyi" domin kare 'yancin bil Adama.

Lalle a fili take cewa, suna amfani ne da "ma'aunoni iri biyu" kan irin wannan matakin nuna karfin tuwo, suna kuma tsoma baki kan harkokin yankin Hongkong da na cikin gidan kasar Sin karara. Sakamakon haka, tabbas ne bangaren Sin ya bayyana matukar bakin cikinsa, da kuma nuna adawa da irin wannan matakin da suka dauka.

Tafiyar da harkoki bisa doka, ka'ida ce mafi muhimmanci ga yankin Hongkong. A watan Faburairun bana, gwamnatin yankin musamman na Hongkong na kasar Sin, ta kaddamar da aikin gyara "ka'idoji biyu" da suke da alaka da masu laifi, wadanda ake neman ruwa a jallo, suke kuma zaune a yankin Hongkong. Dalilin da ya sa aka kaddamar da aikin shi ne, a lokacin da ake shari'ar wasu matsalolin mika masu laifi da ake neman ruwa a jallo ga ketare, za a iya magance wasu matsalolin shari'a da suke kasancewa yanzu a cikin dokokin yankin Hongkong, ta yadda za a iya magance kasancewar yankin Hongkog zama "mafaka ko aljannar masu laifi". A lokacin da aka samu ra'ayoyi daban daban, har ma wasu sun yi zanga-zanga, ko an tayar da hankali a yankin, gwamnatin yankin musamman na Hongkong ta yanke shawarar dakatar da aikin gyara doka, ta yadda za ta iya sauraron karin ra'ayoyi daga bangarori daban daban na yankin, domin ciyar da aikin tafiyar da harkoki bisa doka gaba ciki hadin gwiwa.

Amma wasu masu tsattauran ra'ayi ba su daina ba, saboda sun nemi tayar da hargitsi a Hong Kong, da sunan kin yarda da yin kwaskwarima kan ka'idojin 2, a yunkura cimma burinsu na siyasa, wanda ba su so a sani.

To, me kasashen yammacin duniya suka yi? Da ma su kan yi kira da a tafiyar da harkoki bisa doka. A daidai wannan lokaci ne suka nuna tausayi ga wadannan masu bore, tare da yin shelar cewa, dole ne a tabbatar da ikonsu na yin zanga-zanga cikin lumana. Ko kasashen yammacin duniya sun manta da matakan da suka dauka domin tinkarar irin wannan hargitsi? Yayin da aka samu hargitsi a kasashensu, 'yan sanda su kan yi amfani da makamai domin kama masu zanga-zanga masu yawa. Yanzu me ya sa kasashen yammacin duniya ba su yi tir da yadda masu boren suka kai hari kan babban ginin hukumar kafa doka a Hong Kong ba? A'a, sun mara wa wadannan masu bore baya a fili.

Abin da kasashen yammacin duniya suka yi bisa sharudda guda 2, ya saba wa dokokin kasa da kasa, da kuma manyan ka'idojin daidaita huldar da ke tsakanin kasa da kasa, ya kuma lahanta ikon mulkin kasar Sin, sa'an nan kuma ya taimakawa mutane su kara sanin cewa, wasu kasashe sun kulla makarkashiya da masu adawa da mahukuntan Hong Kong da sunan "'yancin kai da hakkin dan Adam", sun yi yunkurin kwace ikon tafiyar da harkokin Hong Kong, da kawo illa ga yadda kasar Sin take aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu", a kokarin hana ci gaban kasar Sin.

Jama'ar yankin Hongkong, wadanda suka taba haye wahalhalu da fuskantar mawuyacin hali, ba za su yarda a ta da rikici a Hongkong ba. Bisa matsayinsa na wuri na farko da aka fara gwada manufar kasar Sin ta "Kasa daya amma tsarin mulki biyu", yankin Hongkong na ta samun ci gaba cikin sauri, bayan da kasar Birtaniya ta mayar da yankin ga kasar Sin a shekarar 1997. Kana saurin ci gaban tattalin arzikin yankin yana kan gaba, idan an kwatanta da sauran tattalin arziki masu karfi a duniya. Yankin ya samu nasara a kokarin tinkarar rikicin hada-hadar kudi da ya shafi nahiyar Asiya, gami da wanda ya shafi dukkan kasashen duniya baki daya. Har ma hukumomin kasa da kasa da yawa sun ba yankin Hongkong matsayin tattalin arziki mafi samun 'yanci, da kuma wurin dake iya takara da sauran wuraren duniya a fannin tattalin arziki.

Sa'an nan kafuwar babban yankin mashigin teku na Guangdong, Hongkong da Macao, shi ma ya zama sabuwar damar raya tattalin arziki ga yankin Hongkong. Ganin wadannan abubuwa ya sa wasu kafofin watsa labarai na yankin Hongkong ke bayyana cewa, manufar "Kasa daya amma tsarin mulki biyu" ta ba yankin Hongkong fifiko matuka, domin ta raba ma yankin moriyar da kasar Sin ta samu bisa kokarin raya kasa, gami da tabbatar da hakki da 'yanci na mazauna yankin Hongkong.

Game da shisshigin da sauran kasashe suke ma harkokinta, gwamnatin kasar Sin ta bayyana matsayinta sarai: Batun yankin Hongkong daya ne daga cikin harkokin cikin gida na kasar Sin, saboda haka duk wata kasa, ko kungiya, ko kuma daidaikun mutane, ba su da ikon tsoma baki ciki. Idan wani ya tsaya kan yin shisshigi ga harkokin kasar Sin, to kasar za ta fara mayar masa da martani. Kar a raina karfin kasar Sin wajen kare ikon mulkin kanta, domin kasar na tare da cikakkiyar niyya wajen kula da wannan bangare. Duk wani yunkuri na neman yin shisshigi ga harkokin Hongkong, da ta da rikici a kasar Sin, zai ci tura. (Sanusi, Tasallah, Bello)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China