Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ce ke take tsarin duniya ta hanyar nuna fin karfi
2019-07-24 17:32:16        cri

A kwanakin baya, wasu 'yan kasar Amurka fiye da 100 sun gabatar da wata budaddiyar wasika, inda suka zargi kasar Sin da keta ka'idojin kasa da kasa, da neman ta da zaune-tsaye tsakanin kasashen Amurka da Sin. Hakika kalamansu ba su da gaskiya ko kadan, kuma cike suke da girman kai, da jahilci, gami da nuna bambanci.

Al'amuran da ke faruwa a duniyarmu a yau sun nuna cewa: kasar Amurka, bisa wasu ra'ayoyinta na daukar mataki na kashin kai, da kokarin kare moriyar kanta kawai, gami da tsananin son kai, ita ce ke take tsarin da ka'idojin duniya.

An tabbatar da tsarin duniya na yanzu ne tun bayan da aka kawo karshen yakin duniya na biyu, matakim da ya taimaka wajen kyautata yanayin duniyarmu, musamman a fannin tsaro, inda ta hanyar kafa Majalisar Dinkin Duniya an samu damar kare zaman lafiya da tabbatar da ci gaba a duniyarmu. Sai dai a nata bangare, kasar Amurka na neman maye gurbin MDD wajen zama cibiyar aikin tsaro, don kare matsayinta na kasa daya dilo dake da nuna fin karfi a duniya.

idan Amurka ta fahimci cewa, ba za ta iya cimma burinta bisa tsarin MDD ba, sai ta fara neman lalata tsare-tsaren da ake bi yanzu, a yunkurin tabbatar da yadda take danne kasashe a duniya. Yadda gwamnatin Amurka ta yi barna kan tsare-tsaren duniya ya wuce zaton mutane.

A wani bangare, Amurka ta tayar da takaddamar ciniki a tsakaninta da kasar Sin da kungiyar Tarayyar Turai da wasu rukunoni masu karfin tattalin arziki ta hanyar kara sanya haraji. Kana da gangan ta saba yadda ake tafiyar da hakkokin duniya da aka dora mata a kungiyar ciniki ta duniya, abin da ta yi ya haifar da mummunar illa ga tsarin masana'antun duniya da ka'idojin yin ciniki tsakanin sassa daban daban, bisa tsarin yin ciniki cikin 'yanci.

Haka kuma, Amurka ta janye daga hukumar kare 'yancin Adam ta MDD, yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da wasu kungiyoyin kasa da kasa ko kuma yarjeniyoyin duniya, kana ta hana hukumar makamashin nukiliya ta duniya yin aikinta, tare da dakile gyare-gyaren da ake yi kan kungiyar ciniki ta duniya, sa'an nan tana kokarin tsame kanta daga dukkanin dokokin kasa da kasa.

Tsohon jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya John Robert Bolton ya ce, kasarsa tana iya danne duk wata kasa in tana so. Irin wannan ra'ayin nuna fin karfi a duniya da Amurka take da shi, yana keta dokokin kasa da kasa da lalata zaman doka da oda a duniya. Haka kuma ya sa kasashen duniya sake fuskantar matsalar mulkin danniya, da kara raunata tafiyar da harkokin duniya.

Har yanzu akwai wasu 'yan siyasar kasar Amurka wadanda suka lalata zaman doka da oda a duniya da kin yarda da sauke nauyinsu, amma suna zargin gwamnatin kasar Sin da cewa ta yi biris da zaman doka da oda a duniya. Babban dalilin da ya sa haka shi ne, kasar Sin tana kiyaye zaman doka da oda na duniya karkashin jagorancin MDD kuma bisa tushen kundin tsarin mulkin MDD, ba wai zaman doka da oda na nuna ra'ayin danniya da wasu 'yan siyasar Amurka suke so ba.

Sabo da haka, wannan mataki ya fusata wadannan 'yan siyasa, har ma sun zargi matakan da kasar Sin ke dauka na neman samun zaman lafiya da bunkasuwa, da kiyaye muradunta yadda ya kamata, da ma sa kaimi ga tafiyar da harkokin duniya, a matsayin kalubale ga odar kasa da kasa. Lamarin da ya shaida cewa, ko da yaushe wasu Amurkawa na da ra'ayin mulkin danniya, kuma sun damua da ma tsoron bullar ra'ayin kasancewar bangarori da dama da ma yadda ake nuna adawa da ra'ayinsu na mulkin danniya.

Yadda Amurka ke lalata odar kasa da kasa ya gamu da adawa daga kawanyenta. Firaministan kasar Singapore ya nuna cewa, dalilin da ya sa Amurka ta fi son yin shawarari tare da kasashen da ba su fi ta karfi ba daya bayan daya, shi ne sabo da Amurka ta fi saukin samun moriya ta wannan hanya, idan an kwatanta da hanyar kiyaye tsarin kasancewar bangarori da dama.

Sin tana daya daga cikin kasashen da suka kafa odar kasa da kasa, kana ta samu moriya da kuma tabbatar da odar kasa da kasa, idan aka lalata odar, hakan zai kawo illa ga moriyar kasar Sin.

A sakamakon yanayin kara tabbatar da moriyar manyan kasashen yammacin duniya bisa tsarin odar kasa da kasa na yanzu yana da rashin adalci, a matsayinta na babbar kasa mai daukar alhakinta, kasar Sin tana son taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga yin kwaskwarima kan odar kasa da kasa da tafiyar da harkokin duniya yadda ya kamata. Sin ta gabatar da tunanin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, da shawarar "ziri daya da hanya daya", da nuna goyon baya ga MDD da shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa, da kuma fadada bude kofa ga kasashen waje da sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, hakan ya shaida cewa, Sin ta kiyaye tabbatar shiga a dama da ita da kuma yiwa tsarin odar kasa da kasa na yanzu kwaskwarima

Sinawa na kyamar babakere, kuma ba su son nuna fin karfi a kan wani, kuma ta gabatar da sabbin manufofi ne ba din neman dakile wata kasa ba, amma sabo da inganta tsarin gudanar da harkokin duniya da ake bi, ta yadda kasa da kasa za su tabbatar da cin moriyar juna da samun ci gaba tare.

A halin yanzu duniya na fuskantar manyan sauye-sauye, shin wane irin tsari kasa da kasa ke bukata? hakan na bukatar kasa da kasa su yi shawarwari a kai a maimakon sai wata kasa ta fada sauran kuma su ji. Lokacin babakere da Amurka ke yi a duniya ya zama sthon yayi, wanda kuma zai iya kawo barazana ga tsarin duniya. Ya kamata kasa da kasa su dauki matakai na kiyaye tsarin duniya da ke karkashin tsarin dokokin MDD, ta yadda zai gudana yadda ya kamata. (Masu Fassarawa: Bello, Tasallah, Murtala, Kande, Zainab, Lubabatu daga CRI Hausa)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China