Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka fata ne na al'ummun kasashen biyu
2019-07-04 20:45:59        cri

A jiya Laraba ne aka wallafa wani sako mai take "Idan kasar Amurka ta mayar da kasar Sin abokiyar gaba, za ta samu sakamakon da a hakika ba shi take so ba" a jaridar "The Washington Post" inda aka rubuta wa shugaba Donald Trump da majalisun dokokin kasar Amurka sakon a fili.

Wasu masana da kwararru 95 wadanda suka fito daga fannonin ilmi da aikin diflomasiyya da na soja da kasuwa sun sa hannu kan sakon.

A cikin sakonsu, sun mai da hankulansu sosai kan lalacewar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, suna ganin cewa, lamarin bai yi daidai da moriyar kasar Amurka ba, da ma duk duniya gaba daya.

A yankin Washington, babu wani ra'ayi daya da aka cimma kan goyon bayan manufofin "nuna kiyayya ga kasar Sin daga dukkan fannoni". Wannan sakon ya bayyana yadda Amurkawa suke mai da hankulansu kan yadda dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka take tafe.

Mutane biyar wadanda suka rubuta wannan sako sun hada da farfesa M. Taylor Fravel na jami'ar MIT, da Mr. J. Stapleton Roy, tsohon jakadan kasar Amurka a nan kasar Sin, da Mr. Michael D. Swaine, manazarcin dake aiki a cibiyar nazarin harkokin tabbatar da zaman lafiya ta Andrew Carnegie, da Susan A. Thornton, tsohuwar mai ba da taimako ga sakataren majalisar gudanarwar kasar Amurka, da kuma tsohon farfesa Ezra Vogel na jami'ar Harvarda, wadanda suka kware sosai wajen nazarin dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, da harkokin siyasa.

Sun cimma ra'ayi daya da sauran shahararrun mutane 95 na kasar Amurka, wadanda suke wakiltar sana'o'i daban daban na kasar, inda suka yarda da cewa, yadda kasar Amurka ke kallon kasar Sin a matsayin wata abokiyar gaba, ba zai haifar da biyan bukata ba. Wannan ra'ayi na gaskiya ya nuna cewa, 'yan tsirarun masu neman ta da kayar baya tsakanin 'yan siyasan kasar Amurka, suna kokarin ruruta wuta game da yaduwar ra'ayi wai "akwai rikici tsakanin Amurka da Sin", da "ya kamata a katse huldar kasashen 2". Amma sun fadi haka ne domin kwadayinsu na neman moriyar kansu ne kawai, kuma ra'ayinsu ba zai haifar da babban tasiri ga huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ba.

Sa'an nan wannan sakon da aka nuna wa jama'ar duniya ta shaida cewa, yayin ganawar da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka yi a birnin Osaka na kasar Japan a kwanakin baya, sun cimma matsaya wajen ci gaba da kokarin ciyar da huldar dake tsakanin Sin da Amurka gaba, bisa wani tushe na neman daidaita ra'ayoyi, da hadin gwiwa, gami da tabbatar da wani yanayi mai karko. Haka zalika, shugabannin 2 sun yarda da sake komawa teburin shawarwari don neman ganin bayan takaddamar ciniki, matakin da za a aiwatar bisa tushen samun daidaituwa tsakanin kasashen 2, da tabbatar da cewa za su girmama juna. Ra'ayin da shugabannin 2 suka cimma daidaito a kai ya dace da burin da jama'ar kasashen 2 suka sanya gaba, wanda kuma zai biya bukatar gamayyar kasa da kasa.

Daidai da yadda aka bayyana a cikin sakon, kasar Sin ba abokiyar gaba ta kasar Amurka ba ce, musamman ma ta fuskar tattalin arziki. Tushe na huldar dake tsakanin kasashen 2 shi ne manufar neman amfanar juna. Idan wani bangare daga cikin kasashen 2 ya samu nasara, to, ta samu haka ne bisa tushen samun nasara a wani bangare na daban. Amma yanzu matakin karbar karin harajin kwastam da kasar Amurka ke yi ya sabawa tushen, wato ya bata damar tabbatar da amfanin juna, kuma zai haifar da illa ga tattalin arzikin Amurka, gami da na kasar ta Sin.

Alkaluman da ma'aikatar kasuwancin Amurka ta gabatar jiya Laraba sun nuna cewa, a watan Mayun bana ne gibin ciniki na Amurka ya ci gaba da karuwa, har ya kai matsayin koli a watanni 5 da suka wuce, a ciki kuma, gibin ciniki da ke tsakanin Amurka da Sin ya karu da kaso 12.2, inda ya kai dalar Amurka biliyan 30.2 baki daya, hakan ya nuna cewa, kara dora kudin harajin kwastam kan kayayyakin da Sin ke sayarwa a Amurka bai sassauta kulawar Amurka ko kadan ba. Ban da haka kuma, ma'aunin BCI da kamfanin Morgan Stanley ya tsara dangane da yanayin kasuwanci ya ragu zuwa 13 a watan Yuni, a maimakon 45 a watan Mayu, hakan da ake ganin cewa, karfin zuciyar sassa daban daban na Amurka kan yanayin kasuwanci ya raunana cikin hanzari, kana kuma kara dora kudin harajin kwastam kan kayayyakin da Sin ke sayarwa a Amurka ya kawo illa ga hasashen da suka yi kan tattalin arzikin Amurka. Wannan ya shaida mana cewa, Sin da Amurka za su ci gajiya duka idan sun hada kansu, amma za su yi asara duka idan sun yi yaki da juna. Yin hadin gwiwa a tsakaninsu ya fi ta da rikici a tsakaninsu, yayin da yin tattaunawa tsakaninsu ya fi nuna wa juna kiyayya.

Bisa daidaiton da shugabannin kasashen 2 suka cimma yayin taron kolin Osaka na kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki wato G20, an ce, tawagogin kasashen 2 za su tattauna batutuwa filla-filla. Ana bukatar rubanya kokarinsu wajen warware matsala, da kawar da sabani. Idan sun cimma yarjejeniya, to tilas Amurka ta soke dukkan kudaden harajin kwastam da ta kara kan kayayyakin da Sin take sayarwa a Amurka. Muddin bangarorin 2 sun yi tattaunawa cikin adalci tare da nuna wa juna girmama, sun tsaya kan neman moriyar juna, hakan zai haifar da sakamakon da zai gamsar da jama'ar kasashen 2, da kuma samun amincewa daga jama'ar kasa da kasa. (Sanusi, Bello, Tasallah)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China