Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wane ne yake amfani da karfinsa don ci zalin wasu?
2019-07-25 20:00:09        cri

A kwanakin baya ne, wasu Amurkawa fiye da 100 dake kin jinin kasar Sin suka mikawa shugaban kasar Amurka Donald Trump wata wasikar hadin gwiwa, inda suka zargi kasar Sin da neman aiwatar da ra'ayin neman mamaye duniya da yin amfani da karfinta wajen ci zalin wasu. Wannan ra'ayi ba shi da tushe ko kadan.

Da dama daga cikin masu irin wannan tunani na ganin cewa, wasikar za ta dace, idan aka canja kasar Sin zuwa kasar Amurka a cikin wasikar. Wani tsohon hafsan sojojin ruwan yaki na kasar Amurka ne ya rubuta wannan wasika, inda wasu sojojin da suka yi ritaya da masu leken asiri suka sa hannu a kanta. Wadannan mutane ba su da iznin tattauna dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, sun yi hakan ne domin neman suna a duniya.

Alal misali, sun yi ikirarin cewa, a tsarin siyasar Amurka, siyasa harka ce ta yau da kullum, amma yaki abu ne da ba'a amince da shi ba, ba haka lamarin yake ga kasar Sin ba. Wannan ra'ayi ba gaskiya ba ne ko kadan. Manazarta sun ce, tun kafuwar kasar Amurka a shekara ta 1776 zuwa yanzu, kaso 90 bisa dari na shekaru sama da dari biyu da suka wuce, Amurka ta kwashe lokacin tana yaki. A shekara ta karshe cikin wa'adin mulkin Barack Obama, Amurka ta jefa boma-bomai kimanin dubu 26 a kasashe 7. Amma tun kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin har zuwa yanzu, wato a cikin shekaru 70 da suka wuce, kasar Sin ba ta taba tayar da wani yaki ko rikici ba. Don haka, wace kasa ce take kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya?

Hargitsin tsaro da dama da aka tayar a fadin duniya a cikin 'yan shekarun da suka gabata, suna da alaka da kasar Amurka: Inda ta yi amfani da dalilai da sunan yaki da ta'addanci wajen tayar da yaki kan kasashen Afghanistan da Iraki, da kai farmakin soja kan kasar Syria, wadanda suka haddasa rasuwar fararen hula da dama, al'amarin da haifar da matsalar 'yan gudun hijira da ta shafi kasashen Turai. Tun lokacin da gwamnatin Amurka mai ci ta kama aiki, ta kara aiwatar da manufar ra'ayin kashin kai, ga misalin: ta amince da Birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila, hakan ya keta kudurin MDD da ra'ayin bai daya da kasashen duniya suka amince da shi, kana ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a dukkan fannoni bisa radin kanta, wanda ya kara tsananta halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, baya ga haka kuma, ta yi watsi da yarjejeniyar hana amfani da makami mai linzami mai cin gajere da matsakaicin zango da ta cimma tare da kasar Rasha, ta yadda aka murkushe tushen tsaro bisa manyan tsare-tsare na duniya. Duk matakan da kasar Amurka ta dauka sun nuna cewa, kasar Amurka dake nuna karfin tuwo a matsayin makamanta, ita ce wadda ta murkushe zaman lafiyar duniya, kana mai tayar da tashe-tashen hankula a duniya.

Alkaluman da cibiyar nazari ta SIPRI ta fitar sun nuna cewa, a cikin shekarar 2018, a matsayin ta na wadda ke kashe sama da dala biliyan 640 a fannin ayyukan soja, Amurka ce mafi kashe kudade a wannan fannin, sama da jimillar yawan kudaden da kasashe 8 masu biye da ita ke kashewa a wannan fannin.

Gwamnatin kasar Sin ta fitar da sabuwar takardar bayani mai taken "tsaron kasa a sabon zamanin da ake ciki", inda aka bayyana sabuwar sigar musamman ta harkokin tsaron kasar Sin a sabon zamani, wato Sin ba za ta taba neman yin kama-karya ko fadada tasirinta a wasu sassan duniya ba. Haka zalika, takardar bayanin ta yi nuni da cewa, idan an kwatanta kasar Sin da manyan kasashen duniya, za a ga cewa, yawan kudin tsaron kasa da Sin ta kashe a cikin jimillar alkaluman GDP gami da kudaden da gwamnatin ta kashe, da ma matsakaicin kudin tsaron kasar kan ko wane dan kasar duka ba su da yawa. Alal misali, yawan matsakaicin kudin tsaron kasar kan ko wane dan kasar ta Sin ya kai kudin Sin RMB yuan 750 a shekarar 2017, wanda ya kai kaso 5 cikin dari ne bisa na Amurka.

Kalaman tsohon shugaban Amurka mista Jimmy Carter ya dace da abin da mutane suka yi zato, a cewarsa, kasar Amurka, kasa ce dake sha'awar yin yake-yake a tarihin duniya. Amma kasar Sin ba ta taba kashe koda kwabo a yake-yake ba. Kana kuma firaministan kasar Malaysia mista Mahathir ya ce, kasarsa da Sin suna mu'amala da juna cikin shekaru kusan dubu 2, amma kasar Sin ba ta taba kutsa kai cikin Malaysia ba. Sin ba ta taba fadada tasirinta a wasu sassan duniya ba, kuma ba ta wahal da sauran kasashe ba. Amurka na sha'awar tayar da yake-yake, amma ta shafa wa Sin kashin kajin cewa, kasar Sin kasa ce mai son yin yake-yake.

Sun yi amfani da halin da babban yankin Sin da yankin Taiwan ke ciki a matsayi shaida ga tunaninsu a cikin wasikar, wannan mataki abin dariya ne. Sanin kowa ne cewa, batun Taiwan muhimmin al'amari ne ga kasar Sin, babban yankin Sin na yi iyakacin kokarin dinke kasa waje guda lami lafiya da zuciya daya, amma idan ya zama wajaba, Sin za ta dauki matakin soja don hana sauran kasashe ko wasu 'yan aware na Taiwan su kawo baraka ga kasar, amma kasar Sin ba za ta dauki wannan mataki kan mazauna yankin Taiwan ba ko kadan. Wasu 'yan Amurka na ganin ana daukar wadannan matakan dinkuwar kasa a matsayin matakin cin zarafi da tsorata jama'a, ko shakka babu hakan shisshigi ne kan harkokin cikin gidan kasar Sin.

Wasu 'yan Amurka suna yunkurin shafawa kasar Sin kashin kaji saboda an nuna rashin jin dadi da kin yarda da manufar kama karya da ra'ayoyin kashin kai da Amurka ta dade tana dauka. Kuma sun mayar da kasar Sin a matsayin abokiyar gaba har sun gabatar da tunaninsu cewa, wai Sin tana kawo barazana ga duniya, ta yadda kasar Sin za ta yi galaba wajen ganin Amurkar ba ta iya warware rikicin da yake bullowa a cikin kasarta ba, don ta ci riba.

Tun fil azal kasar Sin kasa ce dake rungumar zaman lafiya da jituwa, don haka ba ta bin hanyar "raya kai tare da danna wasu", maimakon haka tana kokarin kare zaman lafiya a duniya. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura sojojinta na wanzar da zaman lafiya dubu 37 zuwa wurare daban daban na duniya, ta yadda ta zama mamba mai kujera din-din-din a kwamitin sulhu na MDD wadda ta tura mafi yawan sojojin wanzar da zaman lafiya, lamarin da ya sa MDD ke kiranta "kasar dake taka muhimmiyar rawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya a duniya". Sa'an nan cikin kasafin kudin karo-karo MDD, adadin da kasar Sin ke bayarwa ya karu daga kashi 2.053% a shekarar 2005, zuwa kashi 12.005% ashekarar 2019. Kuma kasar Sin ta kan biya dukkan kudin ba tare da wani jinkiri ba. Yayin da kasar Amurka, ko da yake tana ganin kanta kamar "Tafi kowa kasa a duniya", ana binta bashin dala miliyan 381 na gudunmowa da ya kamata ta biya don tallafawa kasafin kudin MDD, gami da bashin dala miliyan 776 na gudunmowa ga aikin wanzar da zaman lafiya, bisa alkaluman kididdgar da aka fitar a ranar 1 ga watan Janairun bana. A cewar Antonio Guterres, babban magatakardan MDD, yawan bashin da ake bin kasar Amurka a fannin kudin tallafawa aikin wanzar da zaman lafiya, ya zarce kashi 1 cikin kashi 3 na daukacin kudin da har yanzu ba a biya MDD ba.

Wannan zamanin da muke ciki na tare da rikici da matsaloli, don haka bil Adama na fuskantar kalubaloli na bai daya. Bisa la'akari da wannan yanayin da muke ciki, akwai kasashen Sin da Amurka su hadin gwiwa da juna, a matsayinsu na kasashen dake kujerun din-din-din a kwamitin sulhun MDD, musamman ma lokacin da suke kula da wasu batutuwa masu alaka da tsaron duniya, misali ayyukan da suka shafi batun nukiliya na kasashen Koriya ta Arewa, da Iran, da yanayin siyasa a yankin gabas ta tsakiya, da dai makamantansu. Saboda haka, idan wasu 'yan siyasar kasar Amurka suka ci gaba da rike tunani na yin babakere da nuna fin karfi a duniya, to, al'ummu masu al'adu na zamani za su yi watsi da su. Hanya mafi dacewa da ya kamata kasar Amurka ta bi, ita ce kawo karshen tunanin yakin cacar baki, da ra'ayi na "yadda wani bangare zai samu riba wani bangare na daban ya yi hasara", gami da kokarin hadin kai da sauran kasashe don tabbatar da zaman lafiya a duniyarmu. (Bilki, Murtala, Zainab, Tasallah, Amina, Bello)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China